Saturday, 10 June 2017

Image result for donald trumpSakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce wajibi ne Ƙasashen Yankin Tekun Fasha su sassauta matakin rufe iyakokinsu da ƙasar Qata, wadda maƙwabtanta suka zarga da goyon bayan ayyukan ta'addanci.
A farkon makon nan ne Kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da kuma Bahrain suka dakatar da harkokin sufuri da diflomasiyya tsakaninsu da Qatar.
Mista Tillerson ya ce matakin kasashen na rufe iyakokinsu da Qatar yana iya haifar da mummunar halin matsin rayuwa ga jama'a.
Kodayake, ya yaba wa Sarkin Qatar kan yadda yake kokarin hana samar wa kungiyoyin masu tada kayar baya kudi, sai dai ya ce ya kamata a kara azama.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya zargi Qatar da daukar nauyin 'yan ta'adda kuma ya bukaci ta daina hakan.
"Mun yanke shawara da Rex Tillerson cewa lokaci ya yi da Qatar za ta daina daukar nauyin masu tsatstsauran ra'ayi," in ji Trump.
Ya ci gaba da cewa "ku daina koya wa mutane kashe wasu mutane... Muna so ku dawo cikin jerin kasashe masu hadin kai."
Sai dai Qatar ta musanta zargin taimaka wa kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayin Islama."

0 comments:

Post a Comment

Powered by Blogger.

Movies

Blogroll

Recent Videos

Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari

Shuagban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai, kuma da zarar likitoci sun ba shi dama zai koma gida domin ci gaba da ayyuk...

statistics

Search This Blog

Subscribe

Video

Recent Posts

Posts

Travel

Sample Text

Fashion

Contact Form

Name

Email *

Message *

Video Of Day

Slider

News

Games

Pages

Popular Posts