Shugaba Buhari Na Shirin Dawowa Nijeriya Kafin A Rufe Filin Jirgin Sama Na Abuja
Rahotonni sun bayyana cewa wasu ma’aikatan shugaba Buhari na kokarin ganin ya shigo Nijeriya kafin a kulle babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, kamar yadda majiyarmu ta Sahara Reporters ta rawaoto.
An sanar da cewa za a rufe filin jirgin ne daga ranar 7 ga watan Maris, 2017 inda zai a kai tsawon makonni shida kafin a bude.
Shugaba Buhari ya tafi kasar Ingila ranan 19 ga watan Junairu domin hutu kuma ya dawo ranan 6 ga watan Fabrairu amma har zuwa yanzu bai dawo ba bisa wasu dalilai suka nuna ceaa likitocinsa sun bukaci ya kara kwanakin hutu.
Amma an samu mishkila game da dawowar tasa, yayin da ya rubuta wasika ga majalisan dokoki cewa ba zai samu damar dawowa ba yanzu bisa ga shawarar likitoci.
Har yanzu dai masu magana da yawin shugaban kasa sun ki bayyanawa 'yan Najeriya irin cutar da shugaba Buhari ke fama da shi.
0 comments:
Post a Comment