Thursday, 15 June 2017

Fadar shugabana kasar Najeriya ta maida martani kan matsayin wadansu sanatocin Amurka biyu na kin amincewa da kudurin shugaba Trump na sayarwa Najeriya da jiragen yaki

Sanatocin da suka hada da Cory Booker na jam’iyar Democrat da Rand Paul na jam’iyar Republican sun bayyana rashin amincewarsu da kudurin shugaba Donald Trump na amincewa a saidawa Najeriya manya manyan jiragen yaki irin na zamani samfurin-A29 Super Tucano.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Kakakin fadar shugaban kasar Najeriya Garba Shehu yace wannan batu ne dake tsakanin majalisar dokokin Amurka da fadar shugaban kasar, Ya bayyana cewa majalisar wakilan Amurka ta gayyaci ministan tsaron Najeriya domin yaje yayi mata bayani. Yace ministan bai sami tafiya ranar Laraba da ta gabata da ake bukata ya bayyana gaban majalisar ba sabili da wadansu matsaloli da suka bullo kai a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.

Sanetocin sun bayyana damuwa dangane da batun ci gaba da keta hakin bil’adama daga sojojin Najeriya, a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka yi misali da harin da rundunar sojin Najeriya ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira dake Rann a Karamar hukumar Kale Balge dake jihar Borno a watannin baya.

Sai sai tun a wancan lokacin, babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadiq Baba Abubakar, ya bayyana harin a matsayin na kuskure a wata hira da Sashen Hausa ya yi da shi a ofishinsa. Ya bayyana cewa, manufarsu ita ce su tabbata sun kare rayukan al’umma da mutuncinsu a matsayinsu na ‘yan adam ba akasin haka ba.

Tun a wancan lokacin shelkwatar rundunar ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai bincika inda aka sami kuskuren.

Kotun kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya ta yi watsi da karar da ke gabanta wadda ake tuhumar shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da laifin kin bayyana kadarorinsa.

A lokacin da yake yanke hukunci, Babban alkalin kotun daukaka karar Danladi Umar, ya ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake masa.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Laraba da safe.

Me yasa kotun ta wanke Sanata Saraki?

An wanke shi ne saboda kotun ta ce babu wata hujja da gwamnatin tarayya, wacce ita ce ta shigar da karar, ta gabatar da zai sa a ci gaba da tuhumar Sanata Sarakin.

Alkali Danladi Umar ya ce shaidun da masu shigar da karar suka gabatar sun bayar da hujjoji masu karo da juna wadanda ba za a iya amfani da su wajen yanke masa hukunci ba.

Alkalin ya kara da cewa rahoton da hukumar EFCC ta gabatarwa kotun ya fi kama da bayanan da aka samu ta hanyar samun bayanan sirri maimakon ainihin bincike na shari'a.

Sai lauyoyi sun yi musu bayani kan abin da ya wakana kafin su yi martani akai.

Dama dai ana tuhumar Sanata Sarakin ne da laifuka 18 a karar da hukumar EFCC ta shigar.

Tun a watan Satumbar 2015 ne aka fara tuhumar Sanata Saraki da laifukan da suka danganci cin hanci da rashawa da kuma kin bayyana kadarorin da ya mallaka, a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Kazalika, ana kuma zarginsa da mallakar kadarorin da suka fi karfin aljihunsa da mallakar asusun ajiyar kudade a kasashen waje a lokacin da yake rike da mukaman gwamna da kuma a matsayin sanata.

Saturday, 10 June 2017

Image result for donald trumpSakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce wajibi ne Ƙasashen Yankin Tekun Fasha su sassauta matakin rufe iyakokinsu da ƙasar Qata, wadda maƙwabtanta suka zarga da goyon bayan ayyukan ta'addanci.
A farkon makon nan ne Kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da kuma Bahrain suka dakatar da harkokin sufuri da diflomasiyya tsakaninsu da Qatar.
Mista Tillerson ya ce matakin kasashen na rufe iyakokinsu da Qatar yana iya haifar da mummunar halin matsin rayuwa ga jama'a.
Kodayake, ya yaba wa Sarkin Qatar kan yadda yake kokarin hana samar wa kungiyoyin masu tada kayar baya kudi, sai dai ya ce ya kamata a kara azama.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya zargi Qatar da daukar nauyin 'yan ta'adda kuma ya bukaci ta daina hakan.
"Mun yanke shawara da Rex Tillerson cewa lokaci ya yi da Qatar za ta daina daukar nauyin masu tsatstsauran ra'ayi," in ji Trump.
Ya ci gaba da cewa "ku daina koya wa mutane kashe wasu mutane... Muna so ku dawo cikin jerin kasashe masu hadin kai."
Sai dai Qatar ta musanta zargin taimaka wa kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayin Islama."
Image result for masari
Gwamnan jihar Katsina Rgh. Hon Aminu Bello Masari ya lashi takobin bayar da kyakkyawan tsaro ga 'yan kabilar Igbo mazauna Katsina, dama duk sauran bakin kabilun dake cikin jihar. Gwamnan ya fitar da sanarwar hakan ne a ta bakin mai taimaka masa ta fannin yada labarai Abdu Labaran, inda ya bayyana cewa kabilar Igbon da ta yi fatsali da gargadin barin Arewa da kungiyar wasu matasan Arewa suka yana ta cewa su koma yankunan su, gwamnatin ya ce gwamnati ta shirya tsab domin bayar da kyakkyawan tsaro ga kowa ba tare da nuna bambancin kabilanci ko addini ko banbancin kasa ba.

Tuesday, 6 June 2017

Who is Arsenal's new signing Sead Kolasinac?
Arsenal ta doke Chelsea, Juventus da kuma Tottenham wajen daukar dan wasa Sead Kolasinac
Manyan kungiyoyi na nahiyar turai sun nuna sha'awarsu akan Dan wasan mai shekaru 23 saboda hazakar da ya nuna a kakar wasan da ta wuce a kungiyarsa ta schalke 04.
Arsenal ta bada tabbacin daukan dan wasan a babban shafinta.
  Dan wasan dan kasar Bosnia and Herzegovina  dan wasa ne na baya wanda yake buga wasa a gefen hagu, yakan kuma buga a tsakiyar fili ko kuma tsakiyar baya.
   da wannan Arsenal dake buga wasa a gasar kwarraru ta england ta fara cefanen yan wasanta tun bacin bude cefanen wasan.
Image resultUwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce mijinta na murmurewa sosai kuma nan gaba kadan zai komo gida daga jinyar da yake yi a kasar Ingila.
Tana magana ne a safiyar Talata bayan da ta dawo daga London, inda ta kai masa ziyarar mako guda.
Wata guda kenan da shugaba Muhammadu Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar zuwa Birtaniya - wacce ita ce tafiyarsa jinya karo na biyu a bana.
Hajiya Aisha ta ce shugaban ya "godewa 'yan kasar kan addu'o'in da suke yi masa da kuma goyon bayan da suke bai wa Mukaddashinsa Yemi Osinbajo".
Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.
Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.
Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba. 
Powered by Blogger.

Movies

Blogroll

Recent Videos

Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari

Shuagban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai, kuma da zarar likitoci sun ba shi dama zai koma gida domin ci gaba da ayyuk...

statistics

Search This Blog

Subscribe

Video

Recent Posts

Posts

Travel

Sample Text

Fashion

Contact Form

Name

Email *

Message *

Video Of Day

Slider

News

Games

Pages

Popular Posts