Tuesday, 11 April 2017

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati EFCC ta sake kama wasu maƙudan kuɗi sakamakon kwarmaton masu fallasa bayanai suka yi a ranar Litinin.
Related image
Jami'an EFCC sun kama kuɗin da suka ƙunshi takardun kuɗaɗen ƙasashe daban-daban a fitacciyar kasuwar Balogun da ke Lagos.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren ya ce kudin sun ƙunshi Yuro dubu 547 da 730 da kuma Fam dubu 21 da 90 da kuma Naira miliyan biyar da dubu 648 da 500.
Jimillar kudin ta kai kimanin Naira miliyan 250.
Kamen ya biyo bayan tseguntawa hukumar EFCC ne game da wasu mutane da ba a bayyana sunayensu da suka yi safarar kimanin Naira miliyan 250 zuwa kasuwar Balogun don canza su.
'Yan canjin da aka kama kudin a wajensu sun ce wani ubangidansu ne ya aiko musu da kudin don canzawa.
EFCC ta ce mutum biyu da ta kama suna taimaka mata a binciken da take yi.
A ranar Asabar cikin makon jiya ma, hukumar EFCC ta ce jami'anta sun kama maƙudan kudi a wani babban shago a birnin Ikko.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce jami'anta sun gano sama da Naira miliyan 448 yashe a cikin shagon, wanda aka dade ba a buɗe ba, bayan an tsegunta mata cewa ana shirin canza kuɗin.
A cewar EFCC, shagon na da tambarin 'yan canji, amma an shafee sama da shekara biyu ba a bude shi ba.
Image result for trump
Shugaban Amurka Donald Trump zai aiwatar da shirin sayar wa da Najeriya jiragen yaki domin ta yaki Boko Haram duk da fargabar da ake nunawa kan batun kare hakkin bil'adama.
Jami'an gwamnatin Amurka sun ce an dauki matakin ne domin karfafa wa dakarun Najeriya gwiwa a yakin da take yi da masu tayar da kayar bayan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 30,000.
Idan cinikin ya tabbata, Najeriya za ta sayi jiragen yaki samfurin Embraer A-29 Super Tucano kan kudi dala miliyan 600.
Ana sa ran Shugaba Trump zai mika bukatar yin hakan a hukumance nan da 'yan makonni ga majalisar dokokin Amurka domin neman amincewa.
Najeriya da Amurka sun kitsa yarjejeniyar ne lokacin mulkin tsohon Shugaba Barack Obama, sai dai ba ta fara aiki ba lokacin.
A watan Janairun bana, wani jirgin saman soji ya yi kuskuren kai hari a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke arewa-maso-gabashin kasar, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Shugaba Trump da takwaransa Muhammadu Buhari sun tattauna batun sayar da makaman ne a wata ganawa ta waya da suka yi a watan Fabrairu.
Gwamnatin Najeriya ta sha cewa yakin da take yi da Boko Haram yana fuskantar cikas daga tanade-tanaden dokokin Amurka.
Amurka ta tura wa Najeriya wasu sojoji wadanda za su taimake ta da shawarwari kan yaki da masu tada kayar bayan.
Sai dai bisa tanadin wata dokar Amurka wadda aka yi wa lakabi da Leahy Law, Amurka ba za ta iya sayar wa Najeriya makamai ba saboda zargin take hakkin dan Adam da ake zargin dakarun kasar da aikatawa, kodayake hanin ya shafi duka kayan aiki ne.
Har ila yau, dokar ta yi hani ga sauran kasashe da kada su sayar wa Najeriya makamai saboda yarjejeniyar da suka kulla da Amurkan.

Wednesday, 5 April 2017


Allah ya yiwa daya daga cikin manyan malaman kasar nan Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos rasuwa yanzunnan a wani asibiti dake kano.
Za'ayi jana'izar sa da misalin karfe 11:00am na safe a masallacin Al'furqan dake Alu Avanu a nasarawa a birnin Kano, kamar yadda shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar damu.
Allah ya gafarta masa. Amin.
Allah ya yiwa daya daga cikin manyan malaman kasar nan Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos rasuwa yanzunnan a wani asibiti dake kano.
Za'ayi jana'izar sa da misalin karfe 11:00am na safe a masallacin Al'furqan dake Alu Avanu a nasarawa a birnin Kano, kamar yadda shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar damu.
Allah ya gafarta masa. Amin.
Related image
Mai martaba Sarki Kano Muhammadu Sanusi II ya soki gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari a kan kalaman da ya yi cewa sabon Allah ne ya haddasa cutar sankarau a jiharsa.
Da yake jawabi a wurin wani taro kan zuba jari da aka yi a Kaduna, Sarki Sanusi ya ce bai kamata mutum mai mukami irin na gwamna ya rika alakanta abin da ya shafi kiwon lafiya da sabon Allah ba.
A cewarsa, "Mutum sama da 200 sun mutu, an tambayi gwamna amma ya ce wai sabon Allah ne ya sanya hakan. Bai kamata a rika yin irin wannan jawabi ba. Wannan kalami da {yari} ya yi bai yi daidai da koyarwar Musulinci ba."
"Idan ba shi da maganin rigakafin sankarau, sai kawai ya je ya nemo", in ji mai martaba Sarkin na Kano.
A ranar Talata ne dai Gwamna Abdul'aziz Yari ya ce saɓon Allah da ake yi ne ya jawo annobar sanƙarau da ake fama da ita a ƙasar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya yi jawabin ne bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari a kan batun.
Zamfara ce Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake bai wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.
A makon da ya gabata ne Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar, ta soki gwamnatin Zamfaran a kan gazawarta wajen shirya wa barkewar annobar duk da gargadin da aka rika bayarwa.
A hannu guda kuma gwamna Yari ya ce barkewar annobar ba zai rasa nasaba da rashin biyayyar da mutane ke yi wa Allah ba a wannan lokaci.
Ya ce, "Mutane sun ƙauracewa Allah kuma ya yi alkawarin cewa idan ka yi ba daidai ba to kuwa zaka ga ba daidai ba, kuma ni dai a iya tunanin na wannan shine dalilin da yasa ake fuskantar wannan annobar".
Gwamnan ya kara da cewa babu yadda za a yi a ce zina ta yi yawa kuma Allah ba zai saukar da annobar da babu maganinta ba.
Ga dai tsokacin da gwamnan ya yi a wata hira da manema labari:
Jamhuriyar Nijar na fama da hare-haren ta'addanci

Babban jami'in kula da hukumar zaman lafiya ta jamhuriyar Niger, Kanar Abu Tarka ya ce akwai sa hannun 'yan kasar wajen kai mata hare-hare da kungiyar 'yan ta'adda ta Mali wato Mujao ke kai wa jamhuriyar.
Ya ce da wasu 'yan Niger da suka tsallaka Mali ake kitsa hare-haren.
Yankin Tillaberi dai na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Mujao, al'amarin da ya sanya gwamnati ta ayyana dokar ta-baci har na tsawon watanni uku.
Tuni dai hukumomin kasar suka yi kira ga mazauna yankin Tillaberi da ke iyaka da kasar Mali da su bai wa jami'an tsaro hadin-kai ta hanyar sanar da su duk wata bakuwar fuska da suka gani.
Hukumomin sun ce nuna bakin fuskokin, zai taimaka wajen yaki da ta'adancin da kasar ta sa a gabanta.
Gwamnan jihar Tillaberi, Ibrahim Kachalla wanda ya yi wannan kira, ya ce yankin na fama da hare-haren sari-ka-noke daga 'yantawaye na kasar Mali.
Jamhuriyar Niger dai na tsaka mai wuya sakamakon hare-hare daga kasashe masu makwabtaka da ita.
Kungiyar Boko Haram daga Najeriya da kuma Mujao da ke Mali na kai wa jamhuriya munanan hare-hare da ke sanadiyyar mutuwar mutane da jami'an tsaron kasar.
Powered by Blogger.

Movies

Blogroll

Recent Videos

Ina samun sauki sosai — Shugaba Muhammadu Buhari

Shuagban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana samun sauki sosai, kuma da zarar likitoci sun ba shi dama zai koma gida domin ci gaba da ayyuk...

statistics

Search This Blog

Subscribe

Video

Recent Posts

Posts

Travel

Sample Text

Fashion

Contact Form

Name

Email *

Message *

Video Of Day

Slider

News

Games

Pages

Popular Posts