
Shugaban rikon kwarya na hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Ibrahim Magu, ya ce wadanda ke tsoron kada a fallasu ne suke yakar sa.
A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawan kasar ta ki amincewa da shi a matsayin tabbataccen shugaban hukumar ta EFCC.
Kuma wannan shi ne karo na biyu da majalisar ke kin tabbatar da shi.
'Yan majalisar dai na kafa hujja da cewa sun sami rahoto kan Magu daga hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta kasar dake zarginsa.
Rahoton dai ya nuna Ibrahim Magu na da tabon laifi abin da ke sanya shakku kan yiwuwar yakar cin hanci da rashawa.